Gwamanti ba ta baiwa litikoci kulawar da ta dace-NMA

dakikun karantawa

Kungiyar likitoci ta kasa ta jaddada kudirin ta na hawa kujerar naki kan halin koi in kula kan matakin gwamantin tarayya na rashin baiwa litikoci kulawa duk da cututtuka da suka addabi kasar nan.

Shugaban kungiyar ta kasa Farfesa Innocent AO Ujah ya bayyana hakan, ta bakin shugaban Jihar Kaduna na kungiyar Dakta Sakomba Aliyu ga manema labarai a wani bangaren na bukin shekara-shekara na kungiyar.

Ya ce likitoci na sa kan su cikin damuwa a dai-dai lokacin da suke kokarin kare lafiyar yan Najeriya amma a bangare guda kuma gwamanti na watsi da batun kula da walwalar su.
Sun yi kiran samun karin tagomashi da daga gwamanti domin tsira da mutunci.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da garkuwa da mutane da kuma kisa da ake ma likitoci da sauran jami’an jinya a lokuta daban-daban.
Kuma suka yi kiran daukar matakan gaggawa domin kare lafiya da dukiyoyin membobin so ko’ina suke a fadin kasar nan.

Sanarwar kungiyar ya kuma yi Allah wadai da wasu gwamnatoci jihohi da suke rike da hakkokin likitoci na tsawon lokaci, inda suka ce hakan na haifar da koma baya a bangaren kula da lafiyar majinyata kuma kungiyar ba za ta lamunci hakan ba.

Daga nan sai sanarwa ta yaba ma daukacin likitoci musamman masu aikin kula da lafiyar masu fama da cutar Covid-19 duk da yanayi na hatsari da suke sa kan su ciki, kuma suka yi fatan samun sauyi kan matsalolin da ke damun al’umma a yau.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog