Hukucin Kotu kan karar nadin sabon Sarkin Zazzau

Karatun minti 1

Babbar kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya ta dage sauraren karar da Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu ya shigar yana kalubalantar nadin da aka yi ma sabon Sarkin Zazzau Ambasa Ahmad Nuhu Bamalli zuwa ranar 27 ga watan Oktoban wannan shekara.

 

Kotun wanda mai shari’a Kabir Dabo ke jagoranta, ya ce a wannan rana ce kotu za ta ci gaba da sauraran bangarorin biyu bayan umarnin da kotu ta bayar na mika takardan kara ga wanda ake zargi wato bangarorin gwamantin Jihar Kaduna da Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu da masarautar Zazzau da masu zaben Sarki da kuma shi sabon Sarkin.

 

Masu karar sun garzaya kotu ne suna kalunalantan gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan nadi, inda suka naimi kotun ta yi watsi da shi kuma ta a bi tsarin da aka sani tun shekaru da dama da suka gabata na zaben Sarki a masarautar Zazzau.

 

Bayan an fito daga cikin kotun sai Dabo FM ta tuntubi lauyan masu kara Mai suna Barista Samuel Atum inda ya ce suna wakiltan lauyan Iyan Zazzau ne mai suna Yunusu Ustaz kuma suna kalubalantar matakin da aka bi ne tunda ba’a bi al’adar mutanen Zazzau kuma wanda aka nada bashi cikin wanda masu zaben Sarki suka zaba.

 

Yanzu dai za’a cigaba da sauraron karar ne a ranar 27 ga watan Oktoba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog