Labarai

Gwamna Bala Kaura na jihar Bauchi zai nada Kantomomi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Kaura, ya aikewa majalissar dokokin jihar da sunayen mutane 20 don nada su mukami.

DABO FM tattaro cewa gwamnan gwamnan yana neman sahalewar Majlissar domin nada su mataimakan Kantomomin kananan hukumomin jihar.

Kakakin majalissar, Hon. Abubakar Y. Sulaiman Ningi ne ya karanta takardar a gaban majalissar a zamanta na ranar Talata.

Majalissar ta saka ranar Litinin ta makon gobe a matsayin ranar da zata fara aikin tantance mutanen da gwamnan ya aike mata.

Comment here