Labarai

Gwamnan Borno ya bude shafin da zai dauki manema aiki miliyan 2

Mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya kaddamar da shafin ‘Borno Job Portals’ don daukar ‘yan jihar miliyan 2 aiki.

Gwamnan ya kaddamar da shirin ne a jiya Litinin, 23 ga watan Satumbar 2019 a fadar gwamnatin jihar dake Borno.

Da yake bayyana shirin a shafinshi na sada zumunta, gwamnan Zulum, ya bayyana cewa kaddamar da shirin yana daga cikin manyan kudurorinshi guda 10 na ciyar da jihar gaba.

“Yau, na kaddamar da shafin ‘Borno Job Portal’ wanda zai iya daukar bayanan mutane miliyan 2 wandanda suke neman aiki a daga kananan hukumomi 27 na fadin jihar Borno.

Wannan yana daga cikin kudorinmu guda 10 wadanda muke dasu na ciyar da jihar Borno gaba.”

Comment here