Gwamnan APC ya roki shugaban ‘yan sanda ya cafke Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya aike da wasika zuwa ga shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa, Mohammed Adamu domin rokon yan sanda su chafke sugaban jam’iyyar tasu ta APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa dama dai rikici ya barke cikin jam’iyyar APC ta jihar Edo, tsakanin gwamnan jihar da shugaban jam’iyyar ta APC kuma tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole.

Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar shine ya shaidawa wakilin mu a Abuja a sanyin safiyar Litinin, ya bayyana cewa tini takardar neman shugaban rundunar yan sanda ta kasa ya damke shugaban jam’iyyar APC ta isa ga rundunar yan sandan.

Shaibu ya kuma jaddada wa wakilin Dabo FM cewa zasu kai kwafin takardun kiran damke shugaban jam’iyyar tasu hukumar yan sandan farin kaya tare da hukumomin da abin ya shafa, daga yanzu zuwa ko wane lokaci za’a iya damke Adams Oshiomhole.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.