(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Babu inda Boko Haram take da ko taku daya a Najeriya – APC

Karatun minti 1

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa a duk fadin kasar nan babu inda ke karkashin Boko Haram ko dai dai da inchi guda ne.

Majiyar Dabo FM ta ruwaito mai magana da yawun jam’iyyar Apc, Lanre Issa-Onilu shine ya bayyana hakan a ranar Lahadi, Lanre yace ” Wasu marasa tsoron Allah ne ke kokarin ganin sun haddasa rikici tsakanin musulmi da kirista.”

“Wannan mutane suke fadan maganganun farfaganda akan rashin tsaro tare da shafcin gizo kan Boko Haram, masu garkuwa da mutane dama sauran yan bindiga.”

Ya kara da cewa “A zaben shekarar 2015 da 2019 yan Najeriya sun zabi Shugaba Buhari ne domin ya kawo karshen Boko Haram, haka kuwa akayi.”

“Domin yanzu babu dai dai da inchi guda dake karkashin Boko Haram, masu garkuwa da mutane da sauran yan bindiga a duk fadin Najeriya, kullum fatattakarsu ake ana samun nasara akan su.” Kamar yadda TheCable ta fitar.

Sai dai kuma a dai dai lokacin da kakakin jam’iyyar Apc din yake wannan batu abubuwa sun kara dagulewa a Najeriya, hare haren Boko Haram tare da yawaitar garkuwa da mutane da hare haren yan bindiga yayi tsamari a kasar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog