Labarai

Gwamnati ta dauke Sowore don ta bashi kariya daga masu konashi da wuta – Gwamnati

Fadar shugaba Muhammad Buhari ya bayyana dalilin daya saka jami’an DSS sukayi awon gaba da Omoyere Sowore, dan takarar shugabancin kasa a jami’iyyar AAC.

DABO FM ta tattaro cewa da safiyar ranar Asabar ne dai aka kama Sowore yayin da ake cikin gidanshi a zaune, awanni kadan bayan fara zanga-zangar juyin-juya hali.

Daga cikin hadiman shugaba Buhari akan kafofin sadarwa, Miss Lauretta Onochie, ta bayyana dalilin da ya saka jami’an suka kama Sowore a ranar Asabar.

Da take bayyanawa a shafinta a Twitter, Lauretta tace jami’an sun tafi da Sowore ne domin bashi kariya daga cutar da kanshi idan an fara zanga-zangar daya shirya.

Ta wallafa bayanin ne tare da saka wani hoto inda aka ga hoton wuta tana cinye wani mutumin inda ta rubuta “Hukumar DSS ta tseratar da Sowore daga wannan.”

“Hakkin ne na jami’an tsaro su kare mutane tare da dukiyoyinsu tare da taimaka musu duk lokacin da bukatar hakan ta taso.”

Karin Labarai

UA-131299779-2