Za’a cigaba da kallon shirin ‘Kwana Casa’in’ a watan Oktoba – Arewa 24

Gidan Talabijin na Arewa 24 ta bayyana cewa shirin wasa da take yi na Kwana Casa’in zai cigaba da watan Oktoba.

DABO FM ta binciko daga gidan Talabijin na Arewa 24 wanda har ta wallafa a shafinta na Insatgram.

Tin dai a watan a watan Yuni, Arewa 24 ta tsayar da shirin Kwana Casa’in, wanda a cewarta ta kawo karshen zango farko na cikin shirin.

A watan Yuli kuwa, DABO FM ta gano cewa gidan Talabijin na Arewa 24 ya cigaba da daukar shirin bayan da aka kammala tantance wasu sabbin ‘yan wasa da zasu taka rawa a cikin shiri.

Haka zalika, ‘dan wasan shirin, Abba S Boy ya wallafa wani sako a shafinshi na Facebook inda ya dauki hoto a wajen nadar shirin tare da tabbatar da cigaba da daukan shirin duk dai a watan na Yuli.

%d bloggers like this: