Home LabaraiGwamnatin jihar Jigawa za ta dauki nauyin dalibai domin karatun Likita a kasashen waje

Gwamnatin jihar Jigawa za ta dauki nauyin dalibai domin karatun Likita a kasashen waje

by Hassan M. Ringim
0 comments
Badaru Abubakar

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar zai dauki nauyin dalibai ‘yan asalin jihar Jigawa domin yin karatun Likitanci a kasashen waje.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da DABO FM ta samu daga mataimakin gwamnan a fannin sabbin kafofin labarai, Auwalu D Sankara a yau Alhamis.

Sanarwar ta ce gwamnan ya “umarci ma’aikatar Lafiya karkashin kwaminshinanta Dr. Abba Zakari Umar da su tantance dalibai 60 ‘yan asalin jihar Jigawa masu sha’awar karatun Likita wato ‘Medicine’ domin gwamnati ta dauki nauyin su zuwa karatu kasar waje.”

Kazalika sanarwar ta ce za a dauki daliban daga kowacce mazabar jihar baki daya wadda suke da a kalla ‘5 Credit’ a Biology, Chemistry, Physics, Turanci da kuma Lissafi wadanda kuma suke da shekaru kasa da 23.

Ya kara da cewa; “Wannan shiri na ya yan talakawa ne kawai wadda suka gama karatun Sakandire a makarantun gwamnati kuma za a zakulo daliban bisa chancanta kawai. Ana bukatar daukar a kalla mata 30, maza 30.”

DABO FM ta tattara cewar duk dalibin da yake da sha’awar, zai kai takardunsa zuwa ofishin kwamishinan lafiya na jihar Jigawa daga ranar Juma’a, 3 ga watan Yuli 2020.

Kazalika za a rufe karbar takardu ranar 10 ga watan Yuli inda kuma za a yi jarraba ranar Litinin, 13 ga Yuli 2020.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00