Labarai

Gwamnatin Kano ta dauki kwararru don koyawa Matasan jihar Sana’o’i

Gwamnatin jihar Kano ta dauko kwararru guda 40 daga fannonin Injiniyanci, Zane-zane da sairan fannoni inda zata turasu kasar Birtaniya don daukar horo.

Gwamnatin tace wadannan kwararru 40 da zata tura kasar Birtaniya, zasu dauko hore ne kuma su dawo jihar domin koyawa matasan jihar Sana’o’i daban daban na dogaro da kai.

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ne a bayyyana haka a yayin karbar bakuncin sabbin ma’aikatan hukumar shige da fice da yaye da yayi a ofishinshi.

Dr Nasiru Yusuf Gawuna ne ya wakilci gwamnan yayin ziyarar.

A wata takarda da babban sakataren yada labaran Gawuna, Hassan Musa Fagge ya fitar, ya rawaito mataimakin gwamnan yana cewa; “Babu abinda yafi gina mutane muhimmanci, wannan shine babban dalilin da yasa wannan gwamnatin take ta bada tallafin dogaro da kai.”

“Za’a gastaka haka idan akayi duba akan cibiyar koyarda da sana’o’i da gwamnati ta kammala, wacce za’a bude ta kwanannan.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Bulama, ya bukaci EFFC ta bayyanawa duniya gaskiyar data gano akan bidiyon Ganduje

Dabo Online

Kwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

Dabo Online

Hotuna: Ganduje ya kai ziyara filin da za’a kara rantsar dashi don shiga “Next Level”

Dabo Online

Ganduje ya fara rabon mukamai

Dabo Online

Mutane 30 daga cikin wadanda Ganduje yayiwa aikin ido a unguwar GAMA sun makance

Dabo Online

Ganduje ya bayar da umarnin dinka takunkumin kariya miliyan 1

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2