//
Thursday, April 2

Gwamnatin Kano ta rufe kamfanin kiran Adaidaita Sahu na ‘Opay’

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar yan sandan Najeriya, reshen jihar Kano ta rufe kamfanin Opay a jihar Kano bisa tuhumar rashin cika ka’i’dojin fara aiki a jihar.

Rundunar yan sandan bayyana cewa ta rufe ofishin kamfanin ne biyo bayan rashin cika ka’idar gudanar da aikace-aikacensi a jihar ta Kano.

Ya kuma kara da cewa sun karbi umarnin rufe kamfanin ne daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji.

Gidan Rediyon Freedom ya jihar Kano, ya rawaito cewa;

“Tun da misalin karfe 11 na safiyar ranar Alhamis ne dai jami’an ‘yan sandan suka yi wa ofishin tsinke suka kuma kori dukkanin ma’aikata da masu baburan adal-dai ta sahun.

Masu Alaƙa  #JusticeForKanoKids: 'Yan sanda sun sake kubutar da Yaran Kano 2 daga Anambra

Kana daga bisani suka sanya mukulli suka kulle kofar ofishin, suka kuma girke motocin su a kofar ofishin.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020