Labarai

Kowa na da rawar da zai taka wurin kyautata sha’anin tsaro – Ubangarin Zazzau

An yi kira ga al’ummar yankin karamar hukumar Soba, su cigaba da bin dokokin kasa sau da kafa, tare da sanar da Jami’an Tsaro duk wasu abubuwan da ke faruwa a tsakanin su cikin sauri domin daukar matakan da suka dace saboda tabbatar da doka.

Hakimin Gundumar Soba, kuma Ubangarin Zazzau, Alh Muhammad Bashir Shehu Idris, Shi ne ya yi kiran, sa’ilin da yake tsokaci game da harin da wasu bata gari suka kai a wasu shaguna da ke yankin karamar hukumar, suka kuma yi awon gaba da wasu kayayyaki da dukiya mai tarin yawa.

Dabo FM ta tattaro cewa; Ya kwatanta abun da ya faru, a matsayin sakaci daga wajen al’umma da Jami’an tsaro baki daya, inda ya yi fatan kaucewar sake faruwar hakan a nan gaba.

Hakimin, ya ce, sanar da Jami’an tsaro cikin gaggawa zai taimaka wurin kawo masu dauki a lokacin da ya dace.

Ya kuma Jajantawa Wanda lamarin ya shafa sakamakon aikata ta’asan.

Da ya juya ta bangaren Jami’an tsaron kuwa, ya tunatar da su muhinmanancin da ke akwai gare su, su cigaba da aiki tukuru domin cika alkawarin da suka yi na kare lafiya da dukiyar kowanne dan kasa.

Uban Garin na Zazzau, ya yabawa Gwamnatin Tarayya, da ta Jihar Kaduna, da kuma Majalisar Karamar Hukumar Soba, saboda kokarin da suke koda yaushe na kula da tsaron al’umma.

A daren Lahadin da ta gabata ne dai wasu da ba’a san ko su waye ba, su ka shiga cikin garin na Soba dauke na manyan makamai suka kuma shiga wasu shaguna suka yi awon gaba da kayayyaki na miliyoyin nairori a harin da rundunar ‘yan sandan yankin ta tabbatar da afkuwar sa.

Comment here