Labarai

Gwamnatin tarayya ta sassauta dokar hana zirga-zirga, ta sahale bude masallatai da kasuwanni

JAIPUR RAJASTHAN: Gwamnatin tarayya ta sassuata dokar hana zirga-zirga a Najeriya tare da sahalewar bude guraren bauta a fadin Najeriya baki daya.

Dokar ta koma daga karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba.”

Sai dai tace za a bude ne bisa yadda gwamnatin kowacce jiha ta tsara yadda za a tafiyar da harkokin a jihar.

Shugaban kwamitin yaki da cutar Kwabid19 na Najeriya, Boss Mustapha ne ya sanar da haka a yau Litinin yayi tattaunawa yadda take kasancewa game da cutar a fadin Najeriya.

Kazalika gwamnatin ta amince da bude guraren hada-hadar kudade.

Sai dai tace har yanzu dokar kulle daga karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba ya na nan daram.

Gwamnatin tace har yaznu ba ta amince da haduwar mutane sama da 20 a waje ba, ta hana gidajen abinci da basa cikin otal su yi aiki, sai dai su bude domin ayi tafi da gidanka.

Makarantu, Gidajen rawa, wajen motsa jini, dakunan kallo da wuraren shan giya zasu kasance a rufe har zuwa lokacin da za a bayar da sabuwar sanarwa.

Kalli yadda aka fafata tsakanin sojoji da ‘yan sanda a Zaria.

Karin Labarai

UA-131299779-2