Jarumar shirin ‘Hubbi’, Fadila Muhammad ta rasu

Karatun minti 1

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Fadila Muhammad ta rasu.

Zuwa yanzu ba a sanar da musabbabin mutuwar jarumar ba, sai dai makusantan ta da abokan sana’anta suna ta bayyana jimaminsu game da mutuwar.

Da yake bayyana jimaminsa, jarumi Ali Rabiu Ali wanda aka fi sani da Ali Daddy ya ce; Allah Ya sa Al-kur’ani ya cece ta. Mahaddaciya ce. Allah Ka gafartawa Fadila.”

Maryam Booth: “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Ubangiji Allah Ya jikanki Fadila.”

A wani labarin kuma, DABO FM ta rawaito yadda Ganduje ya amince a zartar da hukuncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi S.A.W a jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Abba Anwar ya fitar da yammacin Alhamis bayan taro da gwamnan ya gabatar a gidan gwamnatin jihar Kano.

“Bazan bata lokaci wajen rattaba hannu akan wannan hukunci da kotu ta yankewa wanda ya yi batanci ga Annabin mu mai girma ba.” inji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Idan baku manta ba kotun shari’ar musulinci ta yankewa mawaki, Sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan tabbatar da samun sa da laifin batanci ga Annabi SAW, wanda ya watsa a kafar Whatsapp a Mayun 2020.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog