Kira ga shugabanni da ‘yan kasuwa kan su tausasawa talakawa – Sheikh Hamza Kabawa

dakikun karantawa

Babban limamin Masallacin Juma’a na Bello Road, Sheikh Hamza Uba Kabawa yayi kira ga shuwagabanni, ‘yan kasuwa da sauran jagororin al’ummar musulmi da suji tsoron Allah SWA su tausasawa talakawa a wannan halin matsi da suke ciki.

Rahoton Dabo FM ya bayyana sakon yazo ne cikin hudubar Juma’a da babban limamin ya gabatar a masallacin juma’a na Bello Road 4 ga Satumbata, inda ya bayyana cewa Manzan Allah SAW yace “Duk wanda Allah ya bawa jagoranci baiyi nasiha ya saukakawa al’umma ba bazai ji kamshin Aljanna ba.”

Shaikh Hamza yayi dogon jan hankali akan muhimmanci na tausasawa ga al’ummar da suke karkashin kowanne irin jagoran ci, “Saukakawa al’umma da tausasawa a cikin maganganun mu da ayyukan mu da ibadar mu da dukkanin masalahar rayuwar mu da alaka tsakanin mu da kanmu da mu’amalar mu sauran alumma.”

Hakika Annabi SAW ya kasance mai saukin hali, ba’a taba bashi wani zabi ba face ya zabi abinda yafi sauki ga alummar sa. Allah yana cewa dashi “Sakamakon wata rahama da Allah ya sanya a zuciyar ka ne ka kasance mai saukin hali da saukakawa alummar ka, da ace ka kasance mai kaushin hali da kowa ya watse daga gare ka, ka zamo mai afuwa ga mutane, ka dinga shawara da alummar ka cikin gudanar da al’amuranka.”

Allah ya umarci Manzon SAW da sassauci, tausasawa, shawara cikin al’amari, sauraron koke koken al’ummar sa wannan shi ake so ga dukkan wani mai shugabantar al’umma. Ana so shugaba ya gujewa dukkan abinda zai zamo tirsasawa, matsawa, takurawa cikin maganganun sa da mu’amalar da zaiyi.

Haka Annabi yaci gaba da wasiyya ga gwamnoninsa su zamo masu saukakawa, ya fada ga sahabbai irin su Mu’az bn Jabal, a lokacin da ya tura su kasar Yaman, yace “Ku zamanto masu saukakawa, kada ku zamanto masu takurawa, ku zamo masu gayawa al’umma abinda zai sa su walwala, kada ku zamanto masu fadin abinda zai takura ko ya bakanta musu rai, ku hade kan ku kuyi aiki tare, kada ku zamanto masu sabani.”

Cikin hadisai da dama Annabi SAW yayi hani da azabtar da koda dabba, yayi hani da sanya dabbobi cikin yunwa, ballantana dan adam. Yanzu duk inda zakaje kowa kuka yake, cikin gida ba dadi waje babu dadi. Idan za’ayi duba da sunayen Allah SWA duk sunaye ne da suke nufin rahama, gafartawa, saukakawa, kuma duk cikin sunayen sa babu wanda yake dauke da matsi ko takurawa.

Don haka nake kira ga dukkan wanda Allah ya bawa jagoranci tun daga kan Shugaban kasa, gomnoni da shuwagabannin kananan hukumomi, shugabannin kasuwa, mutane a gidajen su da ofisoshin su suma su kwatanta suyi kokari su zama sun suffantu da tausayi da saukakawa mutane cikin al’amuran su.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog