(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Hotuna: Yacce wayar Salula ta bata Rayuwarmu ta Yau da Kullum

dakikun karantawa

Wayar Salula aba ce dake taimakawa wajen saukaka rayuwar mutane, wajen neman Ilimi, sada Zumunta dama sauran abubuwan al-fanu.

Sai dai a wani bangaren kuma, tana taimakawa sosai wajen kassara rayuwa, ta hanyar yin wasu abubuwan lalata dangantaka dake tsakanin mutum da Imani da mu’amalar shi.

Wayar Salula, ta kasance mai taimakawa wajen rashin bada cikakkiyar kulawa ga wasu iyayen da suke dirfafar amfani da wayar. Akwai rahotanni da aka samu a kasar Hausa, akwai iyayen da suka kusa salwantar da rayuwan ‘yayansu saboda rashin kula dasu sosai wanda wayar duk ta janyo.

Matsalar har takai wani matsayi data wuce manya, har yara ma bata kyale ba, wasu iyayen suna barin yaransu da basu isa Shari’a ba, rike babbar wayar da zata sahale musu shiga duk wani lungu da sako dake fadin duniya.

Wanda hakan ya iya sawa su shiga wani shafin da ake nuna haramtattun al’amura, yakan hanasu karatu tare da mu’amala da sauran yara.

Hatta ma’auranta ma basu tsira ba, domin tayi sanadiyyar rabuwar aure da dama. Musamman idan aka samu daya daga cikinsu ya kasance mai matsanancin bibiyar shafukan sada zumunta.

Muna fatan mahukunta, tare da iyaye da malamai zasu cigaba da jan hankulan mutane domin cigaba da kaucewa fadawa sharrin wayar salula.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog