Na saka kadarori na a kasuwa domin Ilimantar da Matasa a gida da kasashen waje – Kwankwaso

Engr Kwankwaso yace zuwa yanzu ya saka kadarorin daya mallaka a kasuwa domin ya nemi kudin da zai tura matasa karatu a makarantar gida Najeriya dama kasashen waje.

[adinserter block=”3″]

Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da yayi tare da gidajen rediyo a jihar Kano.

DABO FM ta binciko cewa, Engr Kwankwaso ya bayyana cewa akwai filayen da aka bashi musamman aa jihar Sokoto wanda yace tsohon gwamnan jihar Sen Aliyu Wammako ya bashi.

“Na saka filayen dana mallaka a kasuwa, domin neman kudin da zamu biyawa yaran da mukeson turawa karo karatu a makarantun gida da kasashen waje.”

“Ilmantar da ‘yan jihar Kano ya fiyemin dukkanin kadarorin dana mallaka.”

Masu Alaƙa  Nine Malamin Sanata Kwankwaso a Siyasa - Musa Iliyasu Kwankwaso

“Fili na da yake Sokoto, an saida shi miliyan 35, yanzu haka kudaden suna nan a banki.”

Kwankwaso yace akwai filayenshi dake jihohin Yobe, Adamawa, KAduna da Abuja wadanda a halin yanzu duk suke kasuwa domin neman kudin da gidauniyar zatayi amfani dashi wajen biyawa daliban kudin makaranta kamar yadda DABO FM ta rawaito.

Kwankwaso ya bayyana cewa gidauniyar Kwankwasiyya ta shirya tsaf domin daukar nauyin karatun dalibai 370 domin yin digiri na 2 a kasashen waje.

Yace gidauniyar ta dauki daliban ne wadanda suke da shekarun haihuwa kasa da 30.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

Masu Alaƙa  Budaddiyar wasika ga Dr Rabiu Kwankwaso, Daga Comr. Muzakkir Rabi'u
%d bloggers like this: