Ina siyarwa da masu garkuwa da mutane bindiga akan N30,000 da harsashi N700 – Dillali

Karatun minti 1

A wani sumame da rudunar ‘yan sandan Najeriya reshe jihar Naija ta kame wani dillanin safarar bindigogi da harsasai zuwa ga ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

Rundunar ta samu nasarar cafke dillalin mai suna Ayuba Manta Biyam dan asalin jihar Plateau, mabiyin addinin Kiristanci a kan hanyarshi da yake kokarin yin safarar bindigogi tare da harsashen su.

A wani faifan bidiyon da DSP Hassan Gimba Sule yake yiwa Ayuba tambayoyi domin neman samun bayanai kafin mika shi gaban kotu, Ayuba ya bayyana yacce yake siyar da makaman tare da yin safararsu.

DABO FM ta binciko Ayuba yana amsa tambaya akan nawa nawa yake siyarwa da ‘yan fashi da masu tada zaune tsaya bindigogi.

DABO FM ta tattaro ‘yan sanda sun kame Ayuba tare da bindigogi 2 da tulin harsasai.

Ya bayyana akwai bindigar daya siyar da ita N200,000 da kuma ‘yar N30,000 tare da harsashi akan duk daya N700.

Daga Jaridar Tsakar Gida

Ayuba ya bayyana cewa yana siyo harsashin daga wajen wani ubangidanshi akan N500 inda shi kuma yake kara N200 domin samun ingantuwar kasuwancin shi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog