Bn Uthman-Gumi- Sittu Shawwal
Taskar Malamai

Jahilci ne baƙiƙƙirin wani jahili yace azumin ‘Sittu Shawwal’ ba Sunnah bane – Bn Uthman Kano

Sheikh Muhammad Bn Uthman Kano, babban limamin masallacin Sahaba da ke jihar Kano yace dukkanin wani wanda yace azumin ‘Sittu Shawwal’ bidi’a ne ya fada ne dan jahilci, shubha ko neman suna.

DABO FM ta binciko wani karatun malamin wanda yayi a ranar Juma’a 14 ga watan Yulin 2019 a masallacin Sahaba dake Kundila a jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan karatun Sheikh Dr Ahmad Mahmud Gumi ya ce ‘Azumin Sittu Shawwal ba shi da asali, yin shi Bidi’a ne’

Bn Uthman ya yi ta karanta hadisan tare da lambobinsu wadanda suka tabbatar fahimtarshi da sunnancin Hadisin da yake magana akan azumtar azumin Sittu Shawwal.

“Muslmin ya fitar dashi a hadisi mai lamba ta 1,164, Abu Dawud a cikin sunan mai lamba 2433, Imam Tirmidhi 759, Ibn Majah 1706 da Ahmad Bin Hambal a hadisai masu lamba 23,534, 23,556 da 23,561.”

Sheikh Muhammad ya bayyana cewa jahilice ne baƙiƙƙirin ga ‘wani jahili’ ya fito ya bidi’antar da azumin sittu shawwal bayan ya bayyana cewa a cikin littafin Abdurrahman bn Muhammad, ba Hambale mai suna Al Ihkam shar Usulil Ahkam an rawaice hadisin tare da tabbatar da sunnancin azumin Sittu shawwal, a cewarsa.

“Ashe zai zama jahilici ga wani, kuma jahilci baƙiƙƙirin wani yace wannan azumin (Sittu Shawaal) bidi’a ne.”

“Mun fada saboda an yi wa sunna rashin kunya ne, don haka muke kausasa harshe ga wannan jahilin (Dr Ahmad Gumi), don kusan da wannan.”

“Wannan bashi ne abinda muka san mallam (Abubakar Gumi) ya mutu ya bari akan koyar da addinin musulunci ba.”

“Amma wannnan mai rashin kunyar yake cewa wadannan hadisai sune Imam Malik ya jefa a bola ne.”

Kalli Bidiyo, Daga Shafin Shayk Muhammad Bin Uthman

Karin Labarai

UA-131299779-2