Labarai

Iran tace bada gangan ta harbo jirgin da ya kashe mutane 176 ba

Kasar Iran ta bayyana cewar jami’an tsaronta ne suka harbe jirgin kasar Ukraine da ya fadi a kasar tare da hallaka mutane 176.

Sai dai kasar tace ba da gangan ta harbo jirgin, hakan ya faru ne bisa kuskuren dan adam da kowa zai iya aikatawa.

Tin da farko dai kasar tace bata da hannu a fadowar jirgin, hasalima tace tangardar na’ura aka samu. Tin a rahotanni da cibiyar tsaron Amurka ta Pentagon ta zargi kasar Iran da harbe jirgin cikin kuskure.

Hukumar tsaron kasar ta Iran ta bayyana cewar sune suka harbi jirgin bisa kuskure na tangardar na’urar aiki.

Da take fitar da sanarwar, hukumar tsaron Iran tace “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana bayyana damuwarta da dana sanin wannan kuskuren.”

Shi ma a nashi bangaren, shugaban kasar, Hassan Rouhani ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinshi na Twitter jim kadan bayan da hukumar tsaron ta fitar da sanarwarta.

Shugaban ya kuma mika sakon ta’aziyyarshi ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da bada tabbacin hukunta duk wanda ya aikata kuskuren bayan kammala bincike.

Jirgin dai na dauke da ‘yan kasar Iran su 82, kasar Kanada 63 da sauran kasashe da suka hada da Afghanistan, Jamus da sauransu.

Masu Alaka

Mu muka harbi jirgin Ukraine, bisa kuskure – Jamhuriyar Iran

Dabo Online

Sojojin Amurka 34 sun sami tabin kwakwalwa bayan harin da Iran ta kai musu

Muhammad Isma’il Makama

Rikicin Amurka da Iran zai zama alfanu ga Najeriya ta fannin tattalin arziki – Masana

Faiza
UA-131299779-2