Sarkin kasar Oman, Sultan Qaboos bin Said, mai shekaru 79 a duniya ya rasu kamar yacce kamfanin rarraba labaran kasar da gidajen talabijin a kasar suka tabbatar a ranar Asabar.
“Cikin bakinciki, babbar kotun koli tana jimami… Sarkinmu, Qaboos bin Said….. Allah ya zabar masa barin duniya a ranar Juma’a.
Tini dai kasar ta bayyana hutun kwana 3 domin yin jimamin rasuwar sarkin wanda ya shafe shekaru 50 yana mulkin kasar.
DABO FM ta tattaro cewar tin a shekarar 1970, Sarki Qaboos ya Sarautar kasar wanda shine yake da cikkanen ikon mulkin kasar bayan da ya hambarar da mulkin mahaifinshi.
Hamabarar da a tarihi ta zama mafi kwayu domin babu wanda aka kwarzana balle kaiwa ga mutuwa.
Tin bayan karbar mulkin kasar, ya samar da cigaban da kasar take gani a hali yanzu wanda ya samu kasar a matsayin wuri da babu cigaban zamani musamman a fannin gine-gine da sauran abubuwan zamani.
Sai dai har zuwa rasuwar, Sarkin Qaboos bashi da ‘da magaji, wanda ana sa ran nan da awanni 72 za’ayi nadin sabon Sarkin.
