Home LabaraiIZALA ta tara Naira miliyan 88 na ginin Jami’ar As-Salam a Jigawa

IZALA ta tara Naira miliyan 88 na ginin Jami’ar As-Salam a Jigawa

by Dabo Online
0 comments

Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Ikamatus-sunnah ta sanar da tara Naira miliyan 88 domin ginin Jami’ar mallakin kungiyar a garin Hadeja na jihar Jigawa.

Kungiyar ta fitar da sanarwar a shafinta na Facebook a yau Asabar inda ta bayyana cewa kwamitin tattara kudin ya mika rahotan bayanan kudi zuwa ga shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Baa Lau.

Kungiyar ta ce membobin Izala a fadin Najeriya ne suka hada kudin domin tallafawa ginin jami’ar.

“Kungiyar ta tattara kudin ne daga Jihohin Kasar nan guda 36. Ans amu zunzurutun kudi Naira N86,585,435 daga ‘yan kungiyar dake fadin Najeriya. Shugaba Bala lau ya karbi Rahoton daga hannun shugaban Jibwis na Jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin tattara kudin na kasa.”

DABO FM ta tattara cewar daga cikin mahalarta taron karbar rahotan kwamitin, akwai Sheikh Kabiru Muhammad Gombe, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da sauran manyan malamai na kungiyar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00