/

Amitabh Bachchan da ‘danshi Abishek Bachchan sun kamu da Koronabairas

Karatun minti 1
(H)Abishek Bachchan - (D) Amitabh Bachchan -

Jaipur India (DABO FM) – Fitattun jarumawan Bollywood, Amitabh Bachchan da ‘danshi Abishek Bachchan sun kamu da cutar Kwabid-19, DABO FM ta tabbatar.

Zuwa yanzu an kwantar da jarumawan a asibiti dake birnin Mumbai na jihar Maharastra.

Amitabh Bachchan ne ya fara kamuwa kafin daga bisani sakamakon Abishek ya fito wanda ya tabbatar da cewa shi ma ya kamu da Koronabairas.

Dukkanin jarumawan sun sanar da kamuwarsu a shafukansu na Twitter a a yau Asabar inda Abishek ya sanar da kamuwar a ranar Lahadi, agogon kasar Indiya.

Amitabh ya yi kira da wadanda suka yi hulda da su a kwanakin da basu gaza kai wa 10 ba, su killace kansu.

“Na kamu da Koronbairas. Ina asibiti. Har yanzu muna jiran sakamakon dangi na da kuma ma’aikata. Wadanda mukayi hulda dasu cikin kwanaki 10, ina rokon da su je a yi musu gwaji.

Masana kiwon lafiya sun ce Amitabh Bachchan ya nuna alomomin kamuwa da cutar Koronabairas, ya kuma killace kansa kafin daga bisani ayi masa gwajin cutar, kamar yadda India Today ta rawaito.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Latest from Blog