Limamin canji kuma jagoran talakawa, Mallam Aminu Kano, ya cika shekaru 37 da rasuwa tin bayan da Allah Ya karbi rayuwarshi a shekarar 1983.
Mallam Aminu Kano (1920 – 17 ga Afirilun 1983)
An haifi marigayi Mallam Aminu Kano a 1920, shekaru 40 kafin samun ‘yancin Najeriya. Ya kasance daya daga cikin jagororin da suka nemo ‘yanci talaka a Najeriya daga masu mulkin kama-karya.
Ya kasance malamin addinin Islama, hakan ta sanyashi zama mai bayar da fatawa a bangaren shari’a. Hakazalika malami ne a ilimin Boko wanda ta kai ga ya kafa kungiyar malaman arewa ta farko a tarihi bayan dawowarshi daga makaranta a kasar Burtaniya.
Mallam Aminu Kano ya kasance dan jami’iyyar Mutanen Arewa wacce ta rikide ta koma NPC, ‘National People’s Congress’ kafin daga bisani ya jagoranci bangaren da suka balle daga jami’iyyar zuwa kafa sabuwar jami’iyyar NEPU.
Mallam Aminu Kano ya rasu ranar 17 ga Afrilun 1983.
A Kano, an sanya sunan Mallam Aminu Kano a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Kano, babban asibitn koyarwa dake Kano, babbar kwalejin koyan ilimin addinin Musulunci da Shari’a dake Kano, da sauransu.
