/

Umaru Musa ‘Yar Adua ya cika shekara 11 da rasuwa

dakikun karantawa

Tsohon shugaban Najeriya, Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya cika shekara 11 da rasuwa.

DABO FM ta tattara cewar shugaban ya mutu ne ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2010 bayan fama da matsananciyar rashin lafiya.

Mai bai wa Alhaji Umaru shawara shawara kan harkokin tsaro a wannan lokacin, Janaral Aliyu Gusau ne ya sanar da mutuwar tsohon shugaban a gidan talabijin na NTA, mallakar gwamnatin Najeriya.

Umar ‘Yar Adua, ya kasance tsohon gwamna a jihar Katsina wanda ya yi mulki wa’adi biyu daga shekarar 1999 zuwa 2003, ya yi tazarce daga 2003 zuwa 2007.

Ya kasance gwamna na farko da ya fara bayyana dukkanin dukiyar da ya mallaka kamar yadda dokar Najeriya ta tanada.

Taƙaitaccen tarihin Umaru ‘Yar Adua.

An haifi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951 a garin Katsina.

Mahaifinsa tsohon ministan Lagas ne a jamhuriya ta daya kuma matawallen Katsina, sarautar da marigayi Alhaji Umaru Musa Ƴar Adua ya gada.

Ya shiga makarantar firamari ta Rafukka a shekarar 1958, kuma daga bisani aka mayar da shi makarantar piramari ta kwana da ke Dutsimma.

A shekarar 1965 zuwa 1969 ya yi kwalejin gwamnati ta Keffi.

Daga nan kuma ya tafi kwalejin Barewa, inda ya kammala a shekarar 1971.

Ya shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1972 zuwa 1975, inda yai karatun digirinsa na fannin ilimin koyarwa da na kimiyyar sinadirai.

A shekarar 1978 ne ya koma jami’ar Ahmadu Bellon domin yin digirinsa na biyu a fannin ilimin kimiyyar sinadaren.

Aikin farko da Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya fara shi ne na koyarwa a kwalejin Holy Trinity da ke Lagas a shekarar 1975 zuwa 1976 kuma daga bisani ya koma koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha dake Zaria a tsakanin shekarun 1976 zuwa 1979 ya kuma ci gaba da koyarwa a kwalejin share fagen shiga jami’a ta Zariya har zuwa 1983.

Daga nan ya yi aiki a wurare daban daban.

A lokacin jamhuriya ta biyu ‘Yar Adua ya kasance dan jam’iyyar PRP yayin da a wannan lokacin mahaifinsa ne mataimakin shugaban jam’iyyar NPN na dan wani lokaci.

A lokacin da janar Ibrahim Babangida ke shirin mayar da mulki ga hannun farar hula, Umaru Musa ‘Yar Adua ya kasance daga cikin mutanan da suka kafa wata kungiya mai suna Peoples Front wadda yayanshi Janar Shehu Musa Yar Adua ya jagoranta, kuma ita ce ta rikiɗe ta zama jam’iyyar SDP.

A shekarar 1991, Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar SDP inda ya sha kaye a hannun Sa’idu Barda na jam’iyyar NRC.

‘Yar Adua ya sake tsayawa takarar gwamnan jahar Katsina a shekarar 1999 karkashin tutar jam’iyyar PDP, inda ya yi nasara, an kuma sake zabarsa a shekara ta 2003.

Alhaji Umaru Musa Yar Adua ya kasance gwamna da shugaban kasa na farko a Najeriya da ya fara bayyana kadarorinsa, a wani matakin da wasu ke ganin na yaki da cin hanci da rashawa ne a tsakanin masu rike da maƙaman gwamnati a Najeriya.

Allah Ya yi wa Alhaji Umaru Musa ‘Yar Adua rasuwa ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2010, ya kuma rasu ya bar mace daya Hajiya Turai Yar Adua da ya’ya bakwai, biyar mata biyu maza.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog