Labarai

Bin shawarwarin masana da umarnin gwamnati ya zama dole – Uban garin Zazzau

Uban garin Zazzau kuma hakimin gudumar Soba Alhaji Muhammad Bashir Shehu Idris, ya bukaci al’ummar gundumar sa su kasance masu bin umarni da shawar-warin gwamnati da na masana kiwon lafiya musamman game da cutar COVID-19 da ya addabi al’umma a fadin duniya.

Uban garin na Zazzau ya bayyana hakan ne sa’ilin zantawar sa da Dabo FM a fadarsa da ke Soba.

Ya ce, duk lokacin da aka samu wata musiba a gari babu mafita illa a koma a dangana lamarin ga Allah madaukakin Sarki, tunda shi ne kawai mai yaye dukkanin musibu da fitinu da suke damun al’umma.

Ya nuna bakin cikin sa ganin wadda suka kamu da wannan cuta harda mai girma gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-rufa’i, kuma ya yi masa fatan samun koshin lafiya da ma sauran wanda suka kamu da cutar domin cigaba da gudanar da al’amura kamar yadda aka saba.

Ya kara da cewa,tun bayan bullar cutar ta COVID-19,masana kiwon lafiya sun yi ta shawartan al’umma su dauki matakin kare kan su daga balahiran wannan cuta, da suka hada da wanke hannu akai-akai da kaucewa shiga taruwan jama’a da kuma daukan duk wasu matakai da zai zama rigakafin kamuwa da cutar.

Da ya juya ga tallafin kayan abinci da gwamnatin Jihar Kaduna ta samar a wasu kananan hukumomi kuwa, Alhaji Muhammad Bashir Shehu Idris, ya yabawa matakin na gwamnati ne, sai dai ya ce wasu da ke da hakkin rabon kayayyakin sun gaza raba shi bisa ka’idar da gwamnatin ta shimfida. Kuma ya yi fatan fadada shirin zuwa ga sauran kananan hukumomin Jihar Kaduna.

Karin Labarai

UA-131299779-2