Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya
Labarai

Kwamishina ‘Mai Katobara’ na Ganduje ya nuna jin dadi da mutuwar Abba Kyari

Kwashinan ayyuka da lura da gidaje na jihar Kano, Engr Mu’azu Magaji Dan Sarauniya, yayi kalaman da masu fashin baki suka yi wa fassarar ‘Kalaman Farinciki da jin dadi’ bisa mutuwar Mallam Abba Kyari.

A jiya Juma’a ne dai shugaban ma’aikatan gwamnatin tarraya, Mallam Abba Kyari ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Koronabairas.

Kwashinan ya bayyana cewar mutuwar Mallam Abba Kyari, nasara ce har ma ya kira ta da nasarori biyu.

DABO FM ta tattara cewa kwashina Engr Mu’azu Magaji ya yi furucin ne a wani sako da ya wallafa a shafinshi na Facebook a yau Asabar, 18 ga watan Afrilun 2020.

Kwamishinan yayi nuni da cewa, Najeriya ta kubuta daga irin tafiyar da tsarin mulkin da wasu ke ganin Abba Kyari a matsayin shine yake shugabantar Najeriya ba shugaba Muhammadu Buhari ba.

“Nasarori guda 2, Najeriya ta kubuta kuma Abba Kyari ya mutu cikin annoba.”

“MUTUWAR SHAHADA IN HAR DA IMANI MUTUM YA CIKA.”

Abinda kwamishinan ya wallafa a shafinsa na Muaz Magaji a kan Facebook.

Haka zalika yace bai iya munafurci ba, shiyasa ya fito ya fadi abinda yake cikin zuciyarshi.

DABO FM ta tattara cewar Kwamishinan ayyuka na Kano, Engr Muazu Dan Sarauniya, ya kwarance wajen wallafa zantukan da ake yi wa kallon rashin tauna harshe.

Hakan yasa masu amfani da shafukan sada zumunta suke yi masa lakabi da “Kwamishina mai Katobara.”

A kwanakin baya kwamishinan yayi tsoakci kan zuwan Sarkin Kano murabus, Muhammad Sunusi II garin Legas inda yace; “Suna zamansu lafiya, daga saukar sa ya jawo tashin bom.

Ga wasu daga cikin Kalaman da yayi;

Karin Labarai

Masu Alaka

Tsohon kwamishinan Kano da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari, ya kamu da Koronabairas

Dabo Online

Yanzu- Yanzu: Ganduje ya tsige kwamishanan Kano ‘Mai Katobara’ bayan nuna farinciki da mutuwar Kyari

Dabo Online
UA-131299779-2