Home LabaraiJamhuriyar Nijar ta cire shugaban Sojinta bayan hare-hare sunyi tsamari

Jamhuriyar Nijar ta cire shugaban Sojinta bayan hare-hare sunyi tsamari

by Dabo Online
0 comments

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Issoufou, ya tsige shugaban rundunar sojin bayan tsanantar hare haren mayakan ta’addanci.

A ‘yan kwanakin nan, kasar ta fuskancin muggan hare-haren guda biyu da sukayi sanadiyyar mutuwar sojojin a kalla 160.

Gwamnatin tace wannan wani mataki ne domin canza salon da takeyi na yakar mayakan ta’addancin.

Ahmed Mohamed wanda shi ne shugaban rundunar sojin a baya, ya jagoranci rundunar na tsawon shekaru biyu.

A lokacin da yake jagorantar rundunar, an samu karuwar hare-hare matuka a kasar musamman daga kungiyoyin Boko Haram da kuma sauran kungiyoyi da ke da alaka da IS da kuma al-Qaeda irin su ISWAP.

A garambawul din da shugaban kasar ya yi wa rundunar sojin kasar, shugabanni uku ya sauke.

Sun hada da babban sakatare na ofishin ministan tsaro da shugaban hafsoshin sojojin kasar da kuma babban sifeto na sojoji.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00