Labarai

Sati 2 bayan daurin aure, Babban Limami ya gano garjejen ƙato ya aura

Wani babban limami a kasar Uganda, Sheikh Mohammed Mutumba ya gano bada mace aka daura musu aure ba bayan kimanin sati 2 da daura aure.

Dabo FM ta rawaito namijin amaryar mai suna Swabullah Nabukeera yaja hankalin limamin ne a masallacin Kyampisi cikin shigar mata mai daukar hankali, inda nan take limamin yasha alwashin aurar wannan wanda ya badda kama.

Namijin amarya dai yaki bari kememe wani abu ya shiga tsakanin sa da angon limami bayan da yace yana kan al’ada, bayan sati biyu ne asiri ya tonu inda aka gano ciko yake yi a kirji lokacin da wata ‘yar sanda ta chaje namijin amaryar.

Daga karshe dai wannan kato ya bayyana yayi haka ne don cinye yan kudaden limamin, kuma sunan sa na gaskiya Richard Tumushabe. Kamar yadda TheNation ta wallafa.

Wani abun dariya antin namijin amarya tace ita bata san shi a namiji ba saboda saida ya girma yazo ya zauna da ita, don haka ita a mace ta san dan yar uwar tata.

Sheikh Mohammed Mutumba dai shine limamin masallacin Kyampisi Masjid Noor a garin Kayunga, inda tini hukumar masallacin ta dakatar dashi tare da shiga binciken gaggawa.

Karin Labarai

UA-131299779-2