Jami’an tsaro sun shiga farautar wasu akuyoyi 2 da suka yi kokarin sace motar ‘yan sanda da rana tsaka

Karatun minti 1

Hukumar ‘yan sandar kasar Burtaniya ta shiga farautar wasu akuyoyi guda 2 da sukayi kokarin sace motar ‘yan sanda a unguwar Isle of White ido na ganin ido.

Rahoton Dabo FM ya bayyana hukumar ‘yan sandan ta fitar da sanar war a shafukan ta na sada zumunta inda ta bayyana hakan ya faru ne sakamakon wani abun da akayi zargin na fashewa ne wanda aka gano a kusa da wata unguwa mai suna Newton.

Daga nan hukumar ‘yan sandan ta Burtaniya ta kira Royal Navy Explosives Team domin kawo dauki daga garin Portsmouth na cire wannan burbushin bomb da aka yi kiyasin tun na yakin duniya na biyu ne.

Bayan nasarar cire bom din sai ‘yan sanda suka tarar anyi wa motar su barna sai akuyoyi guda 2 dake kanta kamar yadda suka dauki hoton su, kamar yadda kuka gani.

Hukumar ta bayyana tana rokon ko akwai wanda zai iya gane wadannan akuyoyu guda 2 da suka yi musu barna, cikin salon magana domin tini ‘yan sandan sun zargi yaran makotan wadannan unguwanni da wannan aika aika.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog