Gwamna Zulum ya dauki damarar ‘dakile shan miyagun kwayoyi’ a jihar Borno

Karatun minti 1
Babagana Zulum - Gwamnan Borno (APC)

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen dakile shan miyagun kwayoyi a fadin jihar baki daya.

Gwamnan ya bayyana haka yayin taron kona miyagun kwayoyi da hukumomi a jihar suka kama na kimanin Naira biliyan 3 a kan hanyar Mafa.

Kwayoyin sun hada da tabar wiwi, Tramadol, hodar Iblis da sauransu.

Wakilin DABO FM ya hada mana cewa gwamna Zulum ya ce ya kamta gwamnonin arewacin Najeriya su tashi tsaye cikin gaggawa domin dakile mu’amala da ta’ammali da miyagun kwayoyi duba da cewa jihohin Kano, Kaduna, Borno da Niger suna daga cikin jihohin da ke da mafi yawan masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya.

Kazalika gwamnan ya bukaci a rika tura mutane su rika yin gwajin miyagun kwayoyi kamar yadda ake yin na cuta mai karya garkuwa jiki.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog