Labarai

Jami’ar Bayero ta ragewa dalibanta kudin dakunan kwana

Jami’ar Bayero dake jihar Kano ta rage kudaden dakunan kwanan Dalibai ‘yan asalin Najeriya dake karatu da a makarantar.

Jaridar KANO FOCUS ta rawaito cewar a baya jami’ar ta kara kudin dakunan kwanan da kaso dari tare da fitar da wasu sabbin kudaden da daliban zasu biya.

A wata takarda da jami’ar ta fitar a ranar Juma’a tace ta rage kudin dakunan kwanan bisa korafe-korafen da kungiyar dalibai sukayi.

“Bayan zama da tattaunawa an samun matsaya da amintar rage kudi.”

DABO FM ta tattaro cewar daliban ‘yan Najeriya dake karatun digiri na biyu, zasu biya N20,150 maimakon N25,150, daliban kasar wajen masu yin digiri na 2, zasu biya N80,000.

Haka zalika, sanarwar tace an ragewa daliban dake karatun digirin farko, sun samu ragin N2000 daga cikin 10,090 da suke biya a baya.

UA-131299779-2