Labarai

Lauya ya kai gwamnatin Najeriya Kotu bisa bukatar cire rubutun Ajami daga jikin Naira

Wani lauya mai rajin kare hakkin biladama, Chief Malcolm Omirhobo ya mika gwamnatin Najeriya gaban kuliya da bukatar cire rubutun da ya kira Larabci daga jikin tambarin Sojin Najeriya da takardar kudin Naira.

DABO FM ta tattara cewar rubutun da yake jikin Naira da tambarin Sojoji ba larabci bane. Hausar Ajami ce da mutanen Arewacin Najeriya suke amfani da ita kafin zuwan Boko.

Lauyan ya shigar da karar ne da yin korafin guda 2 masu lamba FHC/ABJ/CS/2/2020 DA FHC/ABJ/C’S/3/2020. Ya shigar da Babban Bankin Najeriya, Ministan Shari’ar Najeriya, Rundunar Sojin Najeriya da Ma’aikatar Tsaron Najeriya.

DABO FM ta tattara bukatar da Lauyan yake aike wa kotu kamar haka;

> Yana so kotu tayi fashin baki da karin akan sashi na 10 da 55 na cikin kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 cewar ko doka ta bayar da damar yin rubutun Larabci a jikin takardar Naira.

> Yana bukatar Kotu ta tambayi wadanda yake kara kan ko dokar sashi na 1(1)(3), 10 da 55 na kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayar da damar sanya rubutun Larabci a jikin tambarin Rundunar Sojin Najeriya.

> Yana kuma buktar Kotu tayi bayani bisa sashi na 55 na kudin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 kan cewar Najeriya kasa ce da ba mallakin kowanne addini ba.

> Ya bukaci kotu da tayi bayani kan cewa ko sashin na 55 na kudin tsarin mulkin Najeriya yace yaren Turanci ne kadai amintaccen yare tare da sanya yaren Hausa, Igbo da Yarouba idan ta kama.

> Kotu tayi bayani kan cewa ko sashi na 1(1) ya dora kudin tsarin mulkin Najeriya a saman wadanda yake kara.

Haka zalika ya bukaci kotu ta haramtawa rundunar sojin amfani da na’uyin rubutu da yake da alaka da kowanne addini tare da haramta amfani da rubutun Ajabi wanda ya kira Larabci daga jikin kudaden Naira.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kotu ta ayyana Kungiyar Shi’a a matsayin Kungiyar Ta’addanci tare da haramta ta a Najeriya

Dabo Online

Kotu ta ki amincewa da bukatar ‘Abba Gida Gida’ na karin sunayen shaidu guda 8

Dabo Online

Kotu ta kara baiwa gwamnatin tarayya umarnin sakin Sambo Dasuki

Dabo Online

Kotu ta umarci Buhari ya kwato Kudaden fansho da tsofaffin Gwamnonin da suka zama Ministoci da Sanatoci

Hassan M. Ringim

Yanzu-yanzu: Baza mu yarda da hukuncin kisa ba, zamu daukaka kara -Lauyoyin Maryam Sanda

Muhammad Isma’il Makama

Kotun karar zaben shugaban Kasa ta yi watsi da karar kalubalantar nasarar Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2