Jarumar barkwanci ‘yar kudancin Najeriya ta yi batanci akan Musulunci

Jarumar barkwanci ta kudancin Najeriya mai suna Gloria Oloruntobi, ta yi maganar batancin akan addinan duniya ciki har da Musulunci.

Oloruntobi ta bayyana haka ne bisa matsayinta da tace yar addinin Kirista ce, inda ta ce babu wani abin bauta a addinin Musulunci, Hindu, Sikh da addinin Buda da yake gaskiya.

DABO FM ta binciko cewa Gloria wacce aka fi sani da Maraji, ‘yar asalin jihar Edo ce, tayi suna da kuma yin fice a shafukan sada zumunta musamman na Instagram wanda a yanzu take da mabiya kimanin miliyan 1 da doriya.

Jaruma Maraji tace; “Hanya daya ce zuwa Aljanna, babu wani Allah (Wal Iyazubillah)-Rubutun Dabo FM, babu wani Buddha, babu wani Krishna na Hindu, babu wani ikirarin asalin dan adam daga Biri, Yesu ne kawai hanya.”

Jaruma ta wallafa bayanan ne a bangaren ‘Story’ na Instagram a tsakar daren ranar Lahadi.

DABO FM ta tattaro cewa; Da take yiwa wasu daga cikin mabiyanta martani a kan sako da suka aike mata na cewa; “Bakya ganin wannan rubutun da kikayi zai zama laifi a wajen Musulmai duk da cewa abin bauta daya muke bautawa?”

Maraji ta yi martani da cewa; “Ba abin bauta daya muke bautawa ba.”

“Shin sun yadda cewa Yesu ‘Jesus’, dan Allah ne? Shin sun yarda cewa mun tsira bisa kammalawar aiki da Yesu yayi na mutuwa a jiki Kuros?

“Shin sun yarda cewa Yesu, shima abin bauta ne? Dukka basu yarda ba ‘yar uwa.

“Kuma zamu samu ceto ne a sakamakon zuwan Yesu, domin yazo ne ya dauke dukkanin laifukanmu kuma ya mutu ne domin mu. Zamu samu ceto ba don Muhammadu (Wal Iyazubillah)-Rubutun Dabo FM , ko Allah ba (Wal Iyazubillah)-Rubutun Dabo FM .

Sai dai Yesu kawai, shi kadai ne hanya.”

Sai dai Jaruma tace ba ta fadi hakan da nufi batawa kowa ba, kawai tana fadar gaskiya ne a cewarta.

Rubutun jarumar ta janyo cece-kuce a shafin Twitter, inda mutane kimanin 50,000 suke magana a kai.

DABO FM ta bincika domin lalubo wasu daga ciki maganganun da mutane ke yi a shafin na Twitter, kama daga masu goyon bayanta har zuwa wadanda suka kurkureta.

Fassara: Idan an samu masu kin aminta da lamirin addininka. Ka tuna Suratul Ikhlas.

DABO FM ba ta goyon bayan mai zagi ko cin mutuncin addinai, musamman addinin Islama.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.