Chelsea ta sai Christian Pullisic daga Borussia Dortmund.

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund dake kasar Jamani ta tabbatar da siyar da dan wasan zuwan kungiyar kwallon kafa ta chelsea dake kasar Ingila.

Chelsea ta sai dan wasan mai shekara ashirin akan kudi  ‎fam miliyan sittin (£60m)  kwatankwacin naira biliyan ashirin da bakwai, miliyan dari bakwai da talatin da takwas, dubu dari biyar da talatin da hudu, da naira dari da ashirin da shida da kobo ashirin da uku (₦27,738,534,126.23).

Christian Pullisic dai zai cigaba da zama a kungiyar Dortmund a matsayin dan wasan aro zuwa karshen kakar wasanni bana ta 2018/2019.

Dan wasan dai yana daya daga cikin matasan yan wasa masu hazaka fa fadin duniya duk da ya samu rasa samu gurbi a kungiyar ta Dortmund masu jan ragamar gasar Bundesliga ta kasar Jamani.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.