Home LabaraiJune 12: Mun gaza farantawa yan Najeriya -Atiku ga ‘yan siyasa da masu madafun iko

June 12: Mun gaza farantawa yan Najeriya -Atiku ga ‘yan siyasa da masu madafun iko

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana har zuwa yau matsayinsu na ‘yan siyasa sun gaza sanya farin ciki a fuskokin yan Najeriya.

A wani sako da ya aike na ranar dumukuradiyya ta kasa, wadda aka maida ta ‘June 12’ wato 12 ga Juni girmamawa ga marigayi Abiola, Atiku ya bayyana takaicin sa na gazawar mulkin siyasa ta kowanne fanni.

Atiku ya kara da cewa “Akwai mutane da dama wanda suka bada rayuwar su a kan lallai sai mun samu ‘yancin mulkin dumukuradiyya irinsu Bashorun MKO Abiola wanda domin shi aka sanya 12 Juni ranar tinawa da gwagwarmayar da suka yi don ganin kowanne dan kasa nada damar bada gudummawa.”

“Akwai wasu da yawa kamar Cif Alfred Rewane; wanda shi nake kwaikwayo, ga Tafida Shehu Musa Yar’Adua, Alhaja Kudirat Abiola da dai sauran su, wadannan duk sun bada rayuwar su domin mu samu mulkin dumukuradiyya.”

“Duk da ware wannan rana ta bikin ranar dumukuradiyya sai dai abin bakin ciki shine har yanzu mun kasa gamsar da wanda muke mulka, mun gaza sanya su farin ciki.”

Daga karshe, Atiku ya kuma shawarci gwamnatin Najeriya kan ta gyara kurakuren gudanar da zabe yanda ‘yan Najeriya zasu gamsu su zabi wanda suke so kuma a basu, wannan shi zai sanya a samu chanji mai dorewa.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00