Ra'ayoyi

Ka nada Abdullahi Abbas sarkin Kano, hakan zai kara fito da irin tunanin ka, Daga Dangalan Muhammad Aliyu

Kaicho ga duk wata al’ummar da ta wadatu da shugaba mai girman jiki irin na girma tare da dumbin karancin zurfin tunani da sanin yakamata.

An wayi gari yau a jihar Kano, a dai dai lokacin da harkar Ilimi ta zama abin ƙi ga gwamnatin Kano, Tallafin sana’o’i ga matasa yazama abin
ƙyama ga gwamnatin Kano, Lafiyar ‘yaya mata da kananan yara ta zama abin wulakantawa, gwamnatin ta dauki dambar baiwa wasu ‘yan majalissa kudin fensho na din-din-din hadi da kara kirkiro masaurautu guda 5 a jihar Kano.

Duk da bani da Ilimin tattalin arziki, sai dai nasan manyan kasashe da suka san me sukeyi, basa yin wani abu har sai su fuskanci zai kara bunkasa tattalin arzikin jiharsu ko kasar baki daya.

A ganina tinda mun wayi gari da lamba 1 ɗan karfa-karfa, me zai hana a nada limamin tsiya-tsiya sarkin Kano, tinda abinda gwamnatin tayi fice akanshi kenan. Bata iya ciyar da yara a firamare ba, bata iya habbaka tattalin arzikin jihar Kano ba, bata iya cigaba da biyawa ‘yan uwanmu dake karatu a kasashen waje kudaden da makarantunsu suke binsu ba.

Kano ta taso a matsayin tsintsiya mai madauri daya, inda duk dan Kano, da Kanon kawai yake alfahari, wanda hakan ya sha bam-bam da sauran jihohi inda har gaba take shiga tsakanin mutanen masarauta 2 da tazo a jiha 1.

Misali; Dan masarautar Azare bayaso ace masa dan Bauchi, Ba Katsine baya amsa Ba Dauri, Dan Zazzau baya amsa Kaduna.

Idan har gwamnatin Kano tana da kudin da zata iya amfani dasu wajen biyan wadannan masarautun da kuma baiwa ‘yan majalissunta fansho na din-din-din, meyasa ta gaza kashe dan kalilan wajen inganta lafiyar mata masu juna biyu wadanda kullin suke mutuwa a wajen haihuwa bisa rashin kyakkyawar kulawa?

Au na manta, ashe Lamba daya yace jihar Kano batada kudi fa, kuma gwamnatin baya ta ciyo bashin makudan kudade…..

Ko wata 2 bakayi da kwace zaben mutan Kano ba, maimakon ka yi abinda zai faranta musu, yasa su soka; ayyukan da ka gaza yi a baya, yanzu ka cika, sai ka ɓige da abinda wasu zasu kira da shashanci ko kuma ace girma ba hankali da tunani.

Kuma muna cigaba da gayawa Allah, da YA kwace mulkinmu daga wannan haramtacciyar gwamnati mara daraja ko ta sisin kobo.

Kai da yakamata ka nemi gafarar kanawa, amma sai gashi ka buge da kara bakanta musu har tana so tafi ta lokacin zabe.

Ya kamata gwamnatin Kano ta sake shiri. Ko da yake kamar kumbo kamar kayanta, gwamnatin da yakamata ta fara yakar jahilci tin daga ofis, batayi ba har ta basu dama sune masu saka wa ayi ko a kar ayi.

Allah ya kare jihar Kano ya bamu zaman lafiya, Allah ka mana maganin makiya da azzalumai masu son durkusar da tunanin matasa masu daraja ta hanyar kin baiwa Iliminsu muhimmanci da jefa su a hanyar shaye-shaye.

Karin Labarai

Masu Alaka

Rigar ‘Yanci: Sabon Salo , Gwamnan Jama’a da Gwamnan Shafaffu da Mai, Daga Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online

Rigar ‘Yanci: Abba Gida Gida ko Executive Mai Sinƙe?, Daga A.M. Fagge

Dabo Online

Zaben Kano: Tsaka mai Wuya ga Jami’iyya Mai Mulki, Daga Umar Aliyu Fagge

Dangalan Muhammad Aliyu

Zato Akan Buharin 2015: Nazata Buhari bazaiyi cuta ba, Daga IG Wala

Dabo Online
UA-131299779-2