Champions League: Bayan shafe shekaru 11, kungiyoyin Ingila zasu kara a wasan karshe

Karatun minti 1

Tin shekarar 2008, kungiyoyin Ingila basu sake haduwa a wasan karshe na kofin zakarun nahiyar Turai ba.

Wasan na karshe da kungiyoyin Ingila 2 suka buga shine wasan Chelsea da Manchester United wanda aka buga a Birnin Moscow na shekarar 2008

Biyo bayan cinye kungiyar Ajax da Totteham tayi , ya baiwa kungiyoyin Ingila damar karawa da juna bayan shafe shakaru 11.

Kungiyar Liverpool ta samu nasarar fitar da Barcelona bayan data zura mata kwallaye 4 a filin wasa na Anfield dake kasar ta Ingila.

Satin daya wuce dai Barcelona ta doke Liverpool a filin wasa na Camp Nou da ci 3 da nema, inda Liverpool din tayi ramuwar gayya ta hanyar jefa kwallaye 4 babu ko daya a ragar BArcelona.

Karin Labarai

Latest from Blog