Buhari ya kaddamar da kwamitin cigaban yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kwamiti a yau Laraba, 8/05/2019 domin cigaban yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Soja mai ritaya, Major-General Paul Tarfa ne zai jagoranci kwamatin.

Shugaba Buhari ya kaddamar da kwamitin ne jim kadan kafin zaman majalissar zartarwa ta tarayya (FEC), inda yayi kira da membobin kwamitin su tsaya sunyi aiki tukuru wajen tabbatar da sun sauke nauyin da aka dora musu.

Tin a watan Janairun 2019 shugaba Buhari ya aike da sunayen membobin kwamitin zuwa ga majalissar kasar domin tantancesu da kuma tabbatar da kwamitin.

A watan Afarilun 2019 ne majalissar ta tabbatar da General Tarfa a matsayin shugaban kwamitin tare da Mohammed Alkali a matsayin Darakta mai gudanarwar kwamitin.

Sauran membobin sun hadar da; Musa Yashi, Mohammed Jawa a matsayin Darakta da shugaban kula da shashin kudade, Omar Mohammed, David Kente, wakilin yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Sauran sun hada da; Asmau Muhammad, wakiliyar yankin arewa maso yamma, Benjamin Adanyi, wakilin arewa ta tsakiya; Olawale Oshun, wakilin yankin kudu maso yamma; T.E.O Ekechi, wakilin yankin kudu maso gabas da kuma Obasuke McDonald, wakilin yankin kudu maso kudu.

Others are Asmau Mohammed, member representing North West zone; Benjamin Adanyi, Member representing North Central zone; Olawale Oshun, member representing South West zone; T.E.O Ekechi, member representing South-East and Obasuke McDonald, member representing South-South zone.

Tin watan Oktobar 2016 majalissar dattijai ta amince da kafa kwamitin domin farfado da durkushe war yankin bisa lahanin da ta’addin yan kungiyar Boko Haram tayi a yankin.

Shima a nashi bangaren, shugaba Buhari ya amince kwamitin a shekarar 2017.

%d bloggers like this: