Kaduna: Matar Aure ta maka Mijinta a Kotu bayan kin kusantarta na tsawon shekaru 5

Wata mata mai suna Talatu, ta mika mai gidanta, Nasiru Suleiman, a gaban kotu dake da zamanta a unguwar Magajin Gari na jihar Kaduna.

DABO FM ta tattaro cewa Talatu, mai shekaru 35, ta shigar da karar ne domin neman mijin nata ya sake ta bayan ya shafe shekaru 5 baya kusantarta. -Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya tabbatar.

Talatu, ta fadawa mai shari’a cewa; Mijinta Sulaiman, ya kaurace mata har na tsawon shekaru 5 cif.

Ta kara da cewa Mijin nata yaki saka yaransu guda 6 a makaranta, lamarin daya saka ta sakasu a makarantar da kanta.

Sai dai ta bayyana duk da bashi ya saka su ba, ya cire su daga makarantar bisa dalilin cewa za’a chanza musu abinda yake dorasu a kai.

“Tsawon watanni tara yanzu basa zuwa makaranta.”

“Gidan da muke ciki bashi da kwari. Beraye duk sun addabemu a gidan, Naira 300 kacal yake bani don in ciyar mishi da yara 7.

“Har fita nake in nemo aikinyi domin tallafawa wajen rike gidan, amma sai yake min kallon ina fita yawon karuwanci ne.”

Hajiya Talatu ta kara da cewa; “So nake ya sake ni, gaskiya bazan iya cigaba da zama da shi ba.”

Sai dai a nashi bangaren, Sulaiman, ya karyata zargin da mai dakin nashi take yi, har ma ya kara da cewa;

“Na bar matata(Talatu) da ciki, amma da na dawo take cemin ai ta zubar da cikin domin ita bazata kara haifar wani yaro ba.”

Sulaiman, ya masa batun bayar da N300 da yakeyi bisa dalilin cewa; ya ajiye kayan Abinci a cikin gidan nashi.

Mai shari’a, Mallam Murtala Nasir, ya umarci ma’auratan da suke su sasanta kansu, inda ya kuma dage sauraron shari’ar har zuwa 23 ga watan Satumbar 2019.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: