Labarai

Kamaru: An bawa Atiku Abubakar wa’adin kwana 21 ya koma Kamaru

Wata kugiyar gamayyar kananan kabilun Najeriya tayi kira ga dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya nemi afuwar ‘Yan Najeriya tare da ficewa daga kasar domin komawa kasarshi ta Kamaru.

Kungiyar tace lallai ne Atiku ya fita daga kasar zuwa nan da kwana 21 ko kuma na nemi iznin zama a Najeriya kko nemi zama dan kasar Najeriya.

Hakan ya biyo baya ne bayan jami’iyyar APC ta bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar ba dan Najeriya bane, inda tace Atikun mutumin Kamaru ne.

Gamayyar dai ta zargi Atiku da yiwa ‘yan Najeriya ‘yar burum burum wajen boye gaskiyar asalinshi wanda tace haka ya sabawa doka kuma dole ne ya fito ya nemi afuwar ‘yan Najeriya.

Kungiyar ta bayyana haka ta hannun sakatarenta, Abdulmuminu Hassan, a wani taron manema labarai da yayi a jiya Litini 15/04/19.

Hassan yace yana kyautata zaton tsohon shugaban kasa, Janaral Babangida ya gano hakikanin asalin Atiku, kuma yana ganin shine dalilin daya sa bai bashi jan ragamar rundunar fasa kwauri ta Custom ba.

“Munason amfani da wannan dama domin mun baiwa Atiku umarnin ficewa daga Najeriya, ya koma kasarshi ta Kamaru domin komawa ga dangin shi.”

Daga karshe sun baiwa Atiku shawara daya nemi izinin zama dan Kasar Najeriya ko yan Najeriya zasu yafe masa bisa rike wasu daga cikin manyan mukamai a kasar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Atiku ya bukaci mataimakiyar Buhari ta biyashi miliyan 500 bisa yi masa kazafi

Dangalan Muhammad Aliyu

Atiku ya yi Allah wadai da kamun Abu Hanifa Dadiyata ‘dan Kwankwasiyya

Dabo Online

Yan soshiyal midiya ne suka dora Atiku a keken bera – Femi Adesina

Muhammad Isma’il Makama

Kotun ‘Allah-ya-isa’ ta fatattaki Akitu tun ba’a je ko ina ba

Muhammad Isma’il Makama

Miliyoyin mata sun roki Atiku ya kwance damarar zuwa Kotu

Dangalan Muhammad Aliyu

Facebook ya rufe shafin kamfanin Israila da ya rika watsa farfaganda da yarfen siyasa a kan Atiku

Dabo Online
UA-131299779-2