Siyasa

KADUNA: El-Rufa’i ya ruguje dukkanin Jami’an Gwamnatin Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i ya bawa dukkanin mukarraban gwamnatinshi umarnin rubuta takardar ajiye aiki.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa Gwamna ya bada umarnin ne ga dukkan ma’aikata ‘yan siyasa da suke cikin gwamnatin a cigaba da shirin kafa sabuwar gwamnati a jihar ta Kaduna.

[the_ad_placement id=”content”]

Gwamnan yace dole kowa ya tabbata ya rubuta takardar ajiye aiki kafin ranar 30 ga watan Afirilun 2019.

Majiyoyi sunce sauke jami’an gwamnatin da El-Rufa’i yayi zai taimakawa jihar wajen baiwa ma’aikatar kudi sauke duk nauyin da yake kanta kafin a shiga sabuwar gwamnati.

Haka kuma daga gefe guda gwamnan na nuni da cewa ba kowane jami’i ne zai samu komawa kujerarshi ba.

Saidai sanarwa ta ware wasu kwamishinonin ma’aikata na 8 wadanda babu su a ajiye aikin, sun hada da:

  1. Ma’aikatar Shari’a
  2. Hukumar Zaben jihar ta SIECOM
  3. Ma’aikatar Ruwa
  4. Hukumar Ma’aikata ta Civil Service
  5. Hukumar Tattara kudaden shiga ta FISCAL
  6. Assembly Commission
  7. Peace Commision
  8. Public Procurement Authority.

Sanarwa dai ta kara ware duk wanda baifi watanni 6 yana aiki ba, wanda suka hada da

  1. Babban Mai kula da Asusun jihar
  2. Pricipal Private Sectary

Da sauransu