Tsohon dan Majalissar Tarayya a Kano, Danlami Hamza ya rasu a cibiyar killace masu Korona

Karatun minti 1

Allah Ya yi wa tsohon wakilin karamar hukumar Fagge a majalissar tarayya, Hon Danlami Hamza rasuwa.

Wani makusancin mamacin ya shaida wa DABO FM cewar tsohon dan majalissar ya rasu ne da yammacin yau Lahadi  a cibiyar killace kai da aka ware wa masu Korona da wadanda ake zargi suna dauke da cutar da ke Kwanar Dawaki a jihar Kano.

DABO FM ta tabbatar da cewa tuni aka yi masa Sallah a cikin motar Asibiti ‘Ambulance’ a unguwar Fagge cikin birnin Kano.

Kafin rasuwarsa ya kasance dan majalissa tarayya mai wakiltar karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewar ya wakilci al’ummar karamar hukumar tin daga shekarar 1999 zuwa 2011 karkashin jami’iyyar APP da ANPP.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog