Saudiyya ta haramta aurar da mata ‘yan kasa da shekara 18

Karatun minti 1

Kasar Saudiyya ta haramta aurar da yan mata a kasar wadanda shekarunsu na haihuwa basu kai 18 ba.

Hakan na kunshe a cikin wata takarda ministar shari’ar kasar, Sheikh Dr. Walid Al-Samaani ya aike wa kotunan kasar tin a shekarar 2019.

Sai dai sanarwar ta ce za a iya bari idan an bincike wasu sharadai.

An ware wasu kotuna da za su iya bayar da dama a daura auren idan an yi wani bincike na lafiya iya yin aure tsakanin ma’auratan.

Ta ce idan kotu ta gamsu babu wanda zai cutu idan aka yi auren, za ta iya bayar da lamuni a daura.

Kazalika sanarwar ta ce ta haramta, kai tsaye, auren maza da mata yan kasa shekara 15.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog