Home LabaraiKano: Yan kasuwa sun sake mamaye Titin IBB

Kano: Yan kasuwa sun sake mamaye Titin IBB

by Dabo Online
0 comments

Yan kasuwa a jihar Kano sun sake mamaye titin IBB, ɗaya daga cikin manyan tituna a faɗin jihar Kano.

A zagayen da DABO FM ta yi, ta gane cewar duk dai gyaran titin da gwamnatin jihar Kano ta yi, tare da iyakance wuraren da ta amince a yi kasuwanci, yan kasuwar sun bijirewa umarnin gwamnatin.

DABO FM ta gane cewar har yanzu yan kasuwar su na cike kusan fiye da rabin titin musamman da tsakar rana a lokutan da motoci da kwastomomi su ke kwaranyowa kan titin.

Al’umma da dama su na nuna ɓacin ransu game da yadda yan kasuwar su ke kwaranyowa kan titin domin yin kasuwanci, lamarin da ya kan sa mutane su shafe mintuna masu yawa kafin wuce titin.

Titin IBB ya kasance ɗaya daga cikin tituna mafi cikowa a tsakiyar jihar Kano duba da yadda titin ya ke hanya da ke kai mutane zuwa manyan kasuwannin jihar.

IBB mahaɗa ce da ke sada al’umma da kasuwar Kantin Kwari, Kasuwar Kofar Wambai, Yan Alluluna, Kasuwar Abbatuwa da kuma Kasuwar Ujile ta ‘yan Goro.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00