Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kasar Burundi ta kwace lasisin BBC, ta tsaurara dakatarwa da tayiwa VOA

1 min read

Gwamnatin kasar Burundi ta fara dakatar da BBC da VOA daga watsa shirye-shirye a Burundi a watan Mayu 2018.

Da take sabunta dakatarwar, gwamnatin Burundi ta zargi VOA dayin amfani da Patrick Nduwimana, tsohon darekta wani kamfanin yada labarai mai zama kanshi wanda ya rikide zuwa Bonesha FM.

Mataimakin Darakta a VOA Amanda Bennett, yace ya cika da mamaki bayan ganin wata sanarwa da gwamnatin ta haramtawa ‘yan jaridar kasar bayar da wani labari ko rahoto ga kamfanin VOA da BBC.

Gwamnatin ta dakatar da BBC da VOA na wata shida. Sai dai a ranar 29 ga Maris ne gwamnatin ta janye lasisin BBC tare da kara wa’adin data diba na dakatar da VOA.

Kwamitin kar hakkin ‘yan Jaridu, reshen kasar Burundi ya wallafa a shafinshi na yanar gizo gizo, inda suka bayyana cew, gwamnatin ta haramtawa duk wasu ‘yan Jaridun kasashen waje yada labarai kai tsaye.

Dokar kuma ta haramta duk wani dan Jarida a kasar Burundi yin aiki da kamfanin VOA da BBC.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.