Copyrighted.com Registered & Protected

Rundunar Sojin Najeriya zata ci bashin makudan Kudade

Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Tukur Buratai yace rundunar zata yi kokarin nemawa kamfanin Naira Biliyan 1.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Buratai ya bayyana haka ne a wajen nuna karshen taron mako na shugaban hafsin sojin a sansanin Kabala dake Jaji.

“Tini munyi nisa wajen nemawa kamfanin rudunar naira biliyan 1. Hakan zai dauki lokaci mai tsayi.

“Muna da hannayen zuba jari dayawa da kuma hanyoyi daban daban da muke tarawa rundunar Kudi.”

“Zamu ci bashi domin tallafawa kamfanin, domin tabbatar da burinmu na tashin kamfani da zai rika kerawa rundunar mu motoci masu dauke da makamai.”

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook
Masu Alaƙa  'Yan Kungiyar Boko Haram sun kwashe makamai dake cibiyar binciken Sojoji a Borno.

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: