Babban Labari Labarai

Kyaftin ya sa ‘yan daba sun yi wa takwaranshi Kyaftin dukan kawo wuka

Yanzu haka Jami’an rundunar soji ta makarantar horas da kwaratan soji da ke Zariya sun dukufa wurin binciko gaskiyar lamarin da ya faru tsakanin wasu masu rike da mukaman Kaftin a rundunar sojin Najeriya.

Hayaniyar da aka yi tsakanin jami’in rundunar sojin Najeriya mai mukamin Kaftin mai suna Kaftin Zakari Sani da ke aiki da rundunar Amo a Jihar Bauchi, da wasu yan daba su 6 da yake zargin wani abokin aikin sa Kaftin Alibaba da daukar nauyi ya haifar da cece-kuce tsakanin mazauna yankin hanyar tsohuwar asibiti kusa da Rex Sinima a Sabon garin Zariya ta Jihar Kaduna.

Lamarin dai da ya faru tsakanin Kaftin Zakari Sani da ‘yan dabar da yake zargin abokin aikin sa Kaftin Alibaba da daukar nauyi, ya faru ne a ranar Juma’a 12 ga watan Yuni na wannan shekara da misalin karfe 12 da mintoci na rana.

Cikin zantawar DABO FM ta Kyaftin Zakari Sani a wata ziyara da muka kai gidansu, ya shaida mana cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ne “Kyaftin Alibaba ya zo kofar gidanmu da wasu ‘yan daba 6 a bayan motarshi, suna zuwa suka rufarmin da duka bisa umarnin Kyaftin Ali Baba.”

Ya kara da cewa bai san inda kan shi yake ba har na tsawon lokaci bayan dukan in da yace al’amarin ya faru ne yana cikin jinyar wani mummunar rauni da ya samu a jihar Binuwai yayin wata arangama da Fulanin Daji.

Da DABO FM ta tambaye shi ko mene yake ganin ya haddasa wannan matsalar da yake ganin shi Kaftin Alibaba ne ya jagoranci wannan hari da aka kai masa?

Sai ya ce; “Tun tsawon lokaci bayan rabuwar Kyaftin Ali Baba da tsohuwar matar sa (Wacce kanwa ce a waje na), aka fadamin Kyaftin Ali Baba ya zo gidanmu , ya ci zarafin wandanda ya samu ciki har da mahaifinmu, wanda haka bai min dadi ba.”

Ya bayyana yadda ya yi kokarin samun Kyaftin Akli Baba domin jin bahasin yin haka, yace bai iya samunshi a waya ba domin ya katse dukkanin hanyoyin samunshi, sai daga baya ya sameshi ta kafar Facebook. Inda daga farawar maganarsu ya yi masa barazanar “Idan har ya isa to ka jira ni a gidan nan da awa guda.

Kwatsam kuwa yana zaune a bisa motar sa a kofar gidan su da ke kusa da Rex Sinima, ya zo da rakiyar wadannan mutane kuma ya umarci su yi mashi wannan dukan.

Ya ce yana da shaida mai suna Muhammad Rabi’u wanda ya ji rauni a yunkurin da ya yi na hana su yin aika-aikar.

Sai dai kuma Dabo FM ta tuntubi wanda ake zargin mai suna Kaftin Alibaba Mai aiki da rundunar Amo da yake Bauchi, Ya ce duk da bashi da izinin yin magana da ‘yan jaridu, amma abun da ya sani shi ne ya zo zai wuce ne sai shi Kaftin Zakari ya sanya yara yan bangar siyasa suka rika jifansa, abu da ya hassala shi kenan kuma ya karyata cewar ya buge shi ko ya sa yara su buge shi.

“Na daura alhakin abun da ke faruwa ga matsalar aure da aka samu tsakanina da ‘yar uwar su Zakari da muka rabu saboda wasu dalilai”, a cewar Kaftin Alibaba

Da Dabo FM ta tuntubi hukumar rundunar sojin Najeriya da ke Zariya, inda ta tabbatar mata cewa, zuwa yanzu an bai wa jami’an rundunar ‘Yan sandar sojoji daman gudanar da bincike kan abun da ya faru kuma da zaran sun kammala bincike za su sanar da mu halin da ake ciki da matakin da za su dauka.

Karin Labarai

UA-131299779-2