(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ko Sarkin Kano da Ganduje sun shirya ya kamata a kammala bincike – Barr Abba Hikima

Karatun minti 1

Ina ganin bai kamata kawai dan Sarki da Ganduje sun shirya shikenan maganar zangin almundahanar da ake wa sarki ya bi iska ba. Wannan ba dai-dai bane komai son da muke wa sarki.

Ya kamata ayi bincike na gaskiya har karshe a gama kuma a fadi gaskiya ko akasin zargin da ake wa Sarki. Wannan shine abun da zai hana mutane marasa daraja samun kafar tayarwa sarkin mu da mu hankali.

Amma yanzu karo na biyu kenan, daga sarki ya fadi gaskiya ko yayi wani motsi wanda bai yiwa gwamnati dadi ba sai a karkade fayil din sa asa hukumomi su fara bincike.

Kamata yayi lallai ayi binciken nan idan sarkin yayi laifi to soyayyar mu dashi baza ta hana mu goyi bayan hukunta shi ba.

Idan kuma akayi bincike na gaskiya aka same shi a wanke, to an toshe bakin tsanya kenan. Nan gaba babu wani mutum mara daraja da zai kara taba Sarki.

Hakan zai kara masa daraja kuma muma masu kare sarkin zamu samu nutsuwa da karfin guiwar kare abun da muka gamsu gaskiya ne.

Ina ganin wannan ita ce mafita.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog