Sarkin Kano, Sunusi II ya mayarwa da Ganduje martani a karon farko

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya mayarwa da gwamnatin jihar Kano akan tuhumar da akeyi masa na al-mubazzaranci da kudin masarautar.

DABO FM ta gane cewa sarkin ya bada amsa kamar yadda gwamnatin jihar ta bashi wa’adin awanni 48 daya kare kanshi kafin ta dauki shawarar da hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci ta bayar na dakatar da Sarkin.

A wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren masarautar jihar Kano, Abba Yusuf, mai lamba KEC/CF/FIN/1/162, ya shaidawa gwamnatin cewa maganar tuhumar masarautar akan kashe naira biliyan 3.4 ba gaskiya bane.

“An umarceni dayin magana akan takarda mai lamba SSG/OFF/03/V.I da kuka aiko.”

“Zaku so sanin cewa Naira biliyan daya da miliyan dari takwas da casa’in da uku da dubu dari uku da saba’in da takwas da dari tara da ashirin da bakwai da kobo talatin da takwas (N1,893,378,927.38) ne kadai a cikin asusun masarautar lokacin da aka nada Sarkin Kano.”

“Yana da muhimmanci ka sani cewa Sakataren Masarauta shine yake kula da asusun masarautar ba mai martaba Sarkin Kano.”

Daga karshe DABO FM ta gano ya bayyana godiyarshi bisa damar da gwamnatin ta bayar domin jin ta bakin bangaren masarautar.

%d bloggers like this: